Labaran Nishadi

Nishaɗi: Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya koma yin wakoƙin Soyayya

Fitaccen mawaƙin siyasar nan a Najeriya harma da ƙetare Dauda Kahutu Rarara ya koma taɓa wakokin soyayya.

Dauda Kahutu Rarara

Mawaƙin idan baku manta ba tun a wata uku baya da suka gabata ne aka jiyo fitaccen mawaƙin ya saki wata waka mai taken Aisha.

Wakar ta sami karɓuwa a shafin YouTube a inda ta tara makallata har miliyan daya ba dubu sittin da daya (939k views) a yayin haɗa wannan rahoto. A sauran kafafen sada zumunta ma wakar ta yi fice a inda take da makallata da wadanda sukayi amfani da sautin sama da miliyoyi.

Tun bayan nasarar da wakar ta samu ne a zuƙatan mutane,wakar ta jawo cece kuce a inda wasu ke ganin Aisha Humaira babbar yarinyar sa yayiwa, sai dai da aka ji daga bakunan su sun bayyanawa duniya waƙa ce da aka yita domin wani shiri mai suna A cikin Biyu.

A shekaran jiya ne mawaƙin ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta cewa ya saki wata wakar tashi ta salon soyayya mai suna Jamila,wanda hakan yayi matuƙar jan hankalin masoyan mawaƙin.

Jamila – Dauda Kahutu Rarara

Wakar Jamila kamar yadda sautin waƙar ya nuna an yi ta ne domin taya Jamila murnar zagayowar ranar haihuwar ta.

Ba tare da bata lokaci ba,zaku iya dakko wakar ko kuma kallon ta a bidiyon dake a kasa,ku cigaba da kasancewa damu domin samun labarai da ɗumiɗumin su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!