Labaran Duniya

Zulum Yayiwa “Yan Kato Da Gora Da Mafarauta Kyautar Albashin Wata Guda – Labarai.com.ng

 Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan alawus-alawus na wata daya ga dubban masu aikin sa kai da ke yaki da Boko Haram da suka haɗar da Civilian Joint Task Force wato CJTF da mafarauta a matsayin kyautan karshen shekara.


Gwamnan ya kuma haɗa da ma’aikatan tsaftar mahalli da ke da aikin tsaftace guraren da ƴan tada kayar bayan suka lalata kafin a sake gina su da kuma masu tsaftar muhalli da ke aiki a cibiyoyin gwamnati da hukumomi.Gwamna Zulum ya sanar da wannan albishir ne yayin wani taro a fadar gwamnatin jihar, lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin sassa daban-daban na masu aikin sa kai.


Ya kuma yi musu godiya ta musamman saboda irin sadaukarwar da suke yi wajen kare jihar a rikicin da ta shafe shekara da shekaru tana fama da shi na Boko Haram

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!