Labaran Duniya

Za’a fara shirya film mai suna Haneefa kan ƙaramar yarinyar da aka kashe a Jihar Kano.

Mai shirya fim ɗin, Ali Sa’id ya bayyana cewa a watan Fabarairu ne za’a fara shirya film ɗin mai dogon zango bisa kan yarinyar da aka kashe kwanakin baya a Jihar Kano.

Ya kuma bayyana cewa dalilin shirya film ɗin shine domin wayarwa da mutane kai bisa yadda za su rinƙa saka idanu akan ƴaƴansu domin kaucewa matsala.

Tare da ƙara bayyana cewa, yana so ta dalilin film ɗin a cigaba da tunawa da Haneefa zuwa na dogon loƙaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!