Labaran Duniya
Zaɓen shugaban ƙasa a Nigeria zai gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023. ~A cewar INEC

Hukumar zaɓe ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Yakubu Muhammad ta bayyana ranar 20 ga watan Fabrairu 2023 a matsayin ranar da za’a gudanar da zaɓen Shugaban ƙasa da na ƴan majalisua a Nigeria.
Farfesa Yakubu ne ya bayyana haka sa’o’i kaɗan da suka gabata, yayin wata tattaunawa ta musamman da kwamitin shirya zaɓe a babban birnin tarayya Abuja.
Ya kuma ƙara da cewa, zaɓen gwamnoni da sanatoci zai gudana a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 23.