Labarai

Yaudarata tayi ta dinga tatsar kudadena, Dan Chinan da ya halaka budurwarsa

Geng Quangrong, dan China mai shekaru 47 wanda yake zama a garin Kano ya bayyana dalilin da ya sanya ya halaka budurwarsa, Ummul Kulthum Buhari a ranar Juma’a 16 ga watan Satumba, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda rahotanni su ka nuna, ya halaka budurwar mai shekaru 25 ne a gidan iyayenta da ka Kabuga Quarters, wuraren Dorayi Babba da ke Jihar Kano.

An samu bayani dangane da yadda ya fayyace wa ‘yan sanda dalilinsa na kai wa budurwa, Ummita kamar yadda kawayenta ke kiranta, hari.

Ya ce ya halaka ta ne sakamakon yaudararsa da tayi bayan kwashe lokaci mai tsawo su na soyayya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce dan Chinan ya shiga gidan iyayenta ne ta Katanga.

A cewar Kiyawa, Quangrong ya dinga caccaka mata wuka ne har sai da yaga ta mutu. Ya bayyana yadda mutumin ya ce iyayenta sun yi masa alkawarin ba shi aurenta amma daga baya su ka ki.

Bayan ya kashe mata makudan kudade ne su ka yaudare shi, hakan ya hassala shi ya far mata.

Kiyawa ya shaida yadda tuni aka zarce da Quangrong zuwa hedkwatar ‘yan sanda da ke Bompai inda ake ci gaba da bincike dangane da lamarin.
An samu rahotanni dangane yadda aka birne gawar Ummita a Kano ranar Asabar, 17 ga watan Satumba kamar yadda shari’ar musulunci ta tanadar.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!