Labarai

“Yan Hisbah Sun Cafke Sarauniyar Kyau Ta Najeriya Shatu Garko

 Shugaban hukumar, Sheikh Muhammad Harun Ibn-Sina, wanda ya bayyana hakan a wata hira da BBC, ya ce yin gasar sarauniyar kyau wani nau’i ne na koya wa mata rashin kunya.


Yana bayani ne kwanaki kadan bayan wata matashiya ‘yar jihar Kano, Shatu Garko, ta lashe gasar sarauniyar kyau.


Shatu, mai shekara 18, ta doke zaratan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma’a da dare a Landmark Centre da ke birnin Legas.


Ita ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turance.


Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku

Ibn Sina ya ce “maganar shiga takarar gasar sarauniyar kyau haramun ne…saboda na farko, ana keta alfarmar musulunci a ciki. Sannan ana bayyana al’aura a ciki, ana karfafa gwiwar ‘ya’ya mata su fito ba tare da kunya ba, wato a koya musu rashin kunya”.


Ya ambato wata ayar AlKur’ani mai tsarki da wani bangarenta yake cewa bai kamata mace ta nuna kwalliyarta ba “sai abin da ya bayyana.”


“Sannan su sa mayafi su rufe jikinsu gaba daya, kuma kada su bayyana kwalliyarsu sai ga mazansu ko iyayensu ko ‘ya’yansu… wannan yana nuna cewa illa ce ga ‘ya mace a matsayinta na mumina ta yi irin wannan [gasa],” a cewar Ibn Sina.


Sai dai wasu ‘yan Najeriya suna sukar hukumar ta Hisbah bisa mayar da hankali kan mutane marasa karfi a yayin da take ikirarin tabbatar da tarbiyya.


A watan Agusta shugaban hukumar ya yi kira ga masu yaɗa hotunan ‘yar Sarkin Bichi, Zarah Nasiru Ado Bayero wadda ɗan shugaban ƙasa Yusuf Buhari zai aura a wancan lokacin, da su guji yin hakan “saboda ya saɓa wa Shari’ar Musulunci”.


Wasu suna ganin kamata ya yi shugaban ya nuna kyamarsa Zarah Nasiru Ado Bayero ba kawsai ga masu yada hotunan ba.


Haka kuma a shekarun baya an soki hukumar bisa rashin daukar wani mataki lokacin da aka yi bikin ‘yar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Fatima Ganduje, wadda aka yi zargin ta sanya tufafin da suka bayyana surarta a lokacin.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!