YADDA ZAKA KARE FACEBOOK ƊINKA DA GA HACKERS.

YADDA ZAKA KARE FACEBOOK ƊINKA DA GA HACKERS.
Assalam alaikum barka da wannan lokaci, duba da irin matsalolin da ake samu a shafukan sata zumunta musamman shafin Facebook da Instagram ta yadda wasu ɓata gari ke amfani da basira wajen kwace Account din mutane domin su danfari bayin Allah.
Mutane dayawa na kukan an kwace musu Facebook account an chanja masa suna an cire bayan nan su an dora na wasu, kuma basu san dalilin yin hakan ba. Wannan yasa naga ya dace nayiwa ƴan’uwa bayanin yadda zasu kare kansu ta yadda babu wanda ya isa yayi maka hacking account dinka na facebook ko Instagram ba tare da izinin ka ba ko da yasan password dinka.
2FA (Two Factor Authentication)
Akwai abin ake kira Two Factor Authentication wani Security ne wanda ake kunnawa, akwai shi acikin mafi yawan shafukan sada zumunta wanda idan ka kunna shi barawon account bazai samu damar yi maka hacking ba ko yasan password dinka.
Abinda #2FA yake nufi shine mukulli na biyu wanda zai tabbatar da kaine mai wannan shafin aduk lokacin da ake je yin #Login. Duk lokacin da wani yayi kokarin shigar da bayanan Account dinka domin ya bude idan ka kunna #2FA za’a tura maka sako da numbobin sirri acikin wayarka ko email dinka ya danganta da wanda ka zaba, dole sai an shigar dasu sannan wannan Account zai bude.
YADDA AKE KUNNA 2FA A FACEBOOK.
Da farko zaka shiga cikin #Settings acikin facebook, sai ka shiga ‘Security and Login’, aciki zaka ga inda aka rubuta “Two Factor Authentication” sai ka shiga ciki zaka ga “Your Security Method” sai ka shiga zai nuna maka inda zaka shigar da number wayarka wacce za’a dinga tura maka sako akan ta, sai ka saka Password na Facebook ɗinka zasu nuna maka “Two Factor Authentication is active” shikenan komai yayi dai dai.
Note!!!
Yakamata ka shigar da number da kasan kaine kayi registration na layin saboda bazaka iya Login Facebook ba sai wannan layin yana cikin wayar ka saboda halin faduwar waya Allah ya kare.
Karku mantaanta da yiwa yan’uwa sharing saboda kowa ya ƙaru 🤝
Cc Abdulrahman Master