Yadda Zaka Dakko Bidiyo Daga YouTube Izuwa Wayarka – Labarai.com.ng
Yadda Zaka Dakko Bidiyo Daga YouTube Izuwa Wayarka Daga Auwal Ghali Auwal
Mutane da dama suna yawan tambayata akan cewa,Shin ta yaya zasu iya dakko bidiyo daga YouTube Izuwa wayoyin su.
Da fari abunda mutum zaiyi idan yana bukatar hakan shine;
Na farko zaka dakko wata manhaja (Application) wadda ake kira da Vidmate ko kuma SnapTube.
Zaku iya dakko Vidmate din ta hanyar danna shudin rubutun dake kasa👇👇👇https://m.apkpure.com/vidmate-downloader-hd-live-tv/com.nemo.vidmate/download
Ba’a samun manhajojin (Apks) a shafin Google Playstore sai dai a shafin yanar gizo na AppPure ko kuma sauran shafukan.
Bayan ka dakko manhajojin da muka ambata a sama wato Vidmate ko kuma SnapTube.
Abunda zaka farayi shine zaka shiga cikin YouTube din.
Bayan ka shiga zaka shiga cikin bidiyo din da kake bukatar ka saukeshi izuwa Wayarka.
A jikin bidiyon zakaga inda akayi alamar kibiya wato inda mutum zaiyi sharing din bidiyo din.
Bayan ka danna kibiyar zakaga ta kawo Maka kamar haka wato Shafukan sada zumunta da kake dasu a wayar,sannan kuma zakaga Vidmate din ko kuma SnapTube din.
Bayan ka gani saika danna kan kan Vidmate din ko kuma SnapTube din.
Da zarar ka danna kan manhajar zai kaika cikin manhajar Vidmate din ko kuma SnapTube din,zakaga inda aka rubuta abunda kake son saukewa izuwa wayar taka, shin bidiyo kake son saukewa ko kuma audio ne,saika danna abunda kake so din Wanda yake bidiyo ko kuma audio.
Kuci gaba da kasancewa damu domin sanin yadda zaku dakko bidiyo daga Facebook,TikTok, Instagram da dai sauransu.