Uncategorized

Yadda Zaka Dakko Bidiyo Daga Facebook Izuwa Cikin Wayarka – Labarai.com.ng

 Yadda Zaka Dakko Bidiyo Daga Facebook Izuwa Cikin Wayarka


Kamar yadda kuka sani a baya mun koya muku yadda mutum zai dakko bidiyo daga YouTube Izuwa wayarshi.


Yau kuma zamu koya yadda mutun zai dakko bidiyo ne daga kan shafin Facebook Izuwa Cikin wayarshi.


Da farko abunda zakuyi shine zaku shiga cikin Playstore dake cikin wayoyin ku,daga sama zakuga inda aka rubuta ‘Search’ wato lalube kenan da Hausa.

Sai ku rubuta kamar haka; ‘Facebook Video Downloader’ bayan kun rubuta hakan zaku sami manhajojin (Apks) din sama da dubu.

Saiki zabi kalar da tafiS yi muku.


Daga nan saiku koma kan Facebook din,kan bidiyo din da kuke bukatar ku sauke,zakuga Wani abu kamar haka a jikin bidiyon din.


Saiku danna kanshi, bayan kunyi haka zakuga inda aka rubuta “Copy link” tom saiku danna copy link din.


Bayan kunyi hakan zaku shiga cikin manhajar da kuka dakko a Playstore ne,bayan kun shiga zai nuna muku kamar haka:


Bayan kunyi pasting a take a wajen bidiyo din zai Sauka ya dawo cikin wayar taku.


Kuna shiga cikin gallery ko kuma MX Player din dake bude bidiyo acikin wayar taku,zaku sami abunda kuka dakko din.


Kuci gaba da ziyartar mu domin ganin yadda zaku dakko bidiyo daga Instagram, TikTok da dai sauransu.

Auwal Ghali Auwal

23-10-2021

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!