Uncategorized

Yadda rikicin ta’addanci yayi sanadiyar mutuwar Sojojin Nigeria 337 cikin shekaru biyu kacal. ~Bincike

Wani rahoto da sashin bincike na SB Morgan (SBM) ya wallafa, ya tabbatarda cewa aƙalla ƴan ta’adda sun kashe mutane 570 haɗe da dakarun Sojoji 337 cikin shekaru biyu kacal a Nigeria.

Ƙungiyar ta SBM ita ce ta bayyana wannan bayan bincike na tsanaki da ta gabatar, tare da samun alƙaluma bisa ga ayyukan na ƴan ta’adda daga shekarar 2019 zuwa yanzu a Nigeria.

A cikin waɗanda suka mutu a yaƙi da ta’addancin harda Jami’an sakai na farin kaya wato (CJTF) mutane 29.

An kuma bayyana cewa, yankin Arewa maso gabashin Nigeria musamman Jihar Borno shine yankin da yafi fuskantar hare-haren ƴan ta’adda. Sai kuma Jihar Zamfara da jumullar hari 45 da sauran Jihohin Yobe, Kaduna, Katsina, Kebbi da Sokotto.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!