Yadda aka kama Uba da Ɗansa suna lalata da yarinya mai shekaru 13 a Jihar Osun.
Jami’an tsaron Nigeria NSCDC reshen Jihar Osun sun kamata wani Uba da Ɗansa suna lalata da yarinya ƴar shekaru 13.
Mai magana da yawu sashin Jami’an tsaron wato Abigun Daniel shine ya tabbatar da hakan ga manema labaru ranar jiya Litinin a garin Osogbo babban birnin Jihar Osun.
Jami’an sun sami bayanan sirrane cewa yarinyar ce ta faɗawa wani mutum yadda Kaka da kuma wanda yake a matsayin Mahaifinta suke lalata da ita, daga nan ne aka umarci a kama Uban nata da Kakan.
Yayin bincike, yarinyar ƴar shekaru 13 ta bayyana cewa Mahaifin nata ya ɗauki tsawon shekaru aƙalla biyu yana lalata da ita. Tun bayan rabuwar Mahaifin nata da Mahaifiyarta kuma ya fara lalata da ita.
Yayinda a wasu loƙutan kuma mahaifin Uban wanda yake a Matsayin Kakanta shima yake lalata da ita a boye. a cewar Yarinyar؟
Har’ilayau; Mista Daniel ya bayyana cewa yanzu haka an miƙa al’amarin sashin kula tare da kare haƙƙoƙin Mata da Yara a Jihar ta Osun domin faɗaɗa bincike kafin a ɗauki matakin daya cancanta da mutanen biyu a shari’ance.