Labarai

Wata mata ta shigar da ƙarar mijinta Kotu, bisa zargin cewa yana takura mata da yawan jima’i.

Wata mata mai suna Olamide Lawal, ta roƙi kotu mai zaman kanta a yankin Mapo dake Ibadan Jihar Oyo akan neman tana son mijinta mai suna Saheed Lawal ya sake ta domin yana takura mata da yawan jima’i.

A cikin takardar da ta miƙawa Kotu, Olamide ta kuma zargi mijin nata da shaye-shayen kayan maye.

Ta bayyana cewa, mijin nata ya kasance mashayin giya na tsawon shekaru 14, kuma a duk loƙacin da ya shawo giyar, sai yazo yana bugun ta, tare da tilastawa dole ya kwanta da ita. Don haka baza ta iya cigaba zaman aure da shi ba.

Babban mai shari’a a Kotun, S.M Akintayi ya saurare koken tare da ɗage ƙarar har zuwa 1 ga watan Maris domin fara gudanar da shari’a tsakanin ma’uratan biyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!