Labarai
Wata Kotu a Nijeriya Ta bada umarnin a cire Lasifika a Masallaci bisa damun mutane da karar kiran sallah.

Wata Kotu a Nijeriya Ta bada umarnin a cire Lasifika a Masallaci bisa damun mutane da karar kiran sallah.
Wani mutum makocin masallaci, ya shiga har cikin masallaci da takalmi,ya mikawa limamin masallacin sammacin kotu ,saboda damun sa da yawan kiran sallah da yace anayi a jahar plateau.

Mutumin yace mahaifiyar sa tanada hawan jini,sannan kanwar sa tanada ulcer ,shiyasa idan an kira sallah yake shiga damuwa .
Bayan shafe shekaru uku ana shari’ar,daga karshe kotu ta bayar da umarnin cire Lasifikar masallacin, inda akaje da lauyoyi da ‘yan sanda aka cire. Kamar yadda Jaridar ATP HAUSA ta ruwaito.