LABARINA
Trending

Wannan Ne Dalilin Fitar Nafisa Abudullahi Daga Shirin LABARINA Series

A sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta.

Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira.
Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya.

“Janyewata daga [shirin] a wannan lokaci ya faru ne saboda yawan da ayyuka suka yi mini, ganin cewa hakan ba zai ba ni damar zuwa a dauki shirin na ‘Labarina’ ba.

Ba kamar yadda ake tunani ba, aiki wajen daukar shirin ‘Labarina’ ya kasance wani abin jin dadi, na yi aiki a fayyace tare da masu daukar shirin, da furodusa da ma dukkan wadanda suka shiga wannan babban shiri, kuma ina cike da farin cikin ganin cewa zan bar shirin ba tare da wata tsana ga kowa ba,” a cewar tauraruwar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!