Kwana Casa'in
Wannan Ne Dalilin Cire Salma Daga Shirin Kwana Casa’in,Asiri Ya Tonu Yanzu-Yanzu
Dalilin Cire Salma Daga Shirin Kwana Casa’in:
Mai bada umarnin shirin nan mai dogon zango na Kwana Casa’in ya bayyanawa duniya dalilin cire jaruma Maryuda Yusuf daga cikin shirin.
Ya fada kamar haka “Farko lokacin da muka so mu cigaba da daukar shirin mun tuntubi jarumar akan shin tana da sha’awar cigaba da fitowa a cikin shirin?
Sai kwatsam Jarumar ta bayyana mana cewa wannan karan sai dai muyi hakuri domin kuwa bazata sami damar bayyana acikin shirin ba”.
Sai daraktan ya so yaji dalilin dayasa Salmar ta fadi haka.
Tuni ta fada mishi cewa ” A gaskiya wannan karon bazan sami dama ba saboda wata matsala daga gidan mu”.
Daraktan yace tun daga wannan lokacin basu kara ji daga bakin jarumar ba,hakanne yasa suka maye gurbinta da wata Jarumar ta daban.
Sai dai masu kallon shirin basu ji dadin hakan ba saboda wasu da dama sun bayyana cewa domin Soyayyar da sukewa jarumar ne yasa suke kallon shirin na Kwana Casa’in din.
Zaku iya kallon cikakkiyar hirar da akayi da daraktan ta hanyar danna hoton bidiyo dake kasa 👇👇👇👇
Www.labarai.com.ng