Wannan Dalilin Ne Yasaka Nake Son A Hanayin TikTok A Najeriya ~ Naziru Sarkin Waka

Fitaccen mawakin kuma jarumi a masana’antar shirya finafinai na na Hausa Naziru M Ahmad wanda wasu sukafi sani da suna Naziru Sarkin Waka ya bayyana takaicinsa akan irin halayan da ake yi da kuma irin mugayan dabi’un da akeyi acikin sahar.
Jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram inda yake ganin gwanda a haramta shafin a Najeriya a huta kawai saboda kar kuma abun yazo ya wuce gona da iri.
Mutane da dama na ganin cewa TikTok shi yafi kamata ace an rufe ba Twitter ba.
Haka dai mutane sukaci gaba da bayyana ra’ayoyin su.
Ga duk wanda yake bibiyar shafin ya kwana da sanin yadda har aka daura aure ta sanadiyar shafin tsakain shahararrun “yan TikTok din guda biyu Maimuna Mai Zool da kuma Mawaki Muhammad Zool,dukkan su biyun Hausawa ne mazauna kasar Saudiyya kuma ta sanadiyar shafin sukayi aure har kuma ta sanadiyar shafin suka rabu,wato ya sake ta.
Ba’a jima da sakin ba sauran shahararrun shafin da suke rigima da ita Mai Zool din wato Jamila Suddeenly suka dinga tsokanarta da tada husuma wadda har yanzu an kasa kashe ta.
Sai dai yanzu haka shafin ya cika da maganganu iri-iri bayan da akaga wata budurwa mai suna Aisha Zakky wadda take bangaren dabar Maimuna Mai Zool taje har gidan su Suddenly din da niyar suyi sulhu daga nan ne kuma sukayi mata lilis har suka dauki bidiyo suka dora na dukan nata.
Yanzu haka da ba’aji komai ba daga bakin Suddeenly din ba.
Haka dai rigimgimu suke ta faruwa na Kashe aure da kuma na rashin mutunci duka a shafin.
Wannan Dalilin ne yasaka Naziru Sarkin Waka yayi hangen gwanda a rufe shafin a huta saboda yana lalata tarbiyar matasa masu tasowa.
Allah yasa mudace!