Wani magidanci ya mayar da wallet wadda ya tsinta ɗauke da kusan miliyan ɗaya a Jihar Bauchi.

Wani magidanci mazaunin Jihar Bauchi ya nuna Imani, yayinda ya mayarda jakar kuɗi (wallet) da ya tsinta ɗauke naira dubu 9820.
Wanda ya jefar da wallet ɗin mai suna Bashir Aliyu Limanci ya bayyana cewa kuɗin da suke cikin wallet ɗin sun kusa miliyan ɗaya ga kuma takardu masu matuƙar amfani, amma 1800 kawai bawan Allah ya ɗauka.
Cikin wata ƴar wasiƙa da Ladan ya rubuta bayan mayar da wallet ɗin ga mai ita, ya bayyana Aliyu cewa “nine na tsinci wallet ɗinka, a gaskiya kuma banyi niyyar mayar da ita ba, amma bayan ganin maƙudan kuɗaɗen da suke ciki yasa na sauya shawara, amma daga cikin kuɗin na ɗauki dubu ɗaya da ɗari takwas domin siyawa iyalina masarar tuwo, saboda tsawon kwanaki biyu ba’ayi girki a gidana ba”.
Ganin yadda al’amarin ya ja hankalin musamman ma’abota shafukan sada zumunta, mutane da yawa suna yunƙurin tallafawa wannan bawan Allah bisa irin halin adalcin da ya nuna.