Malam Shehu Dan Iya

Wallahi “Yan Fim Din Hausa Sunfi Malamai Tasiri A Wannan Lokacin – Malam Shehu Dan Iya

 Wasikar Malam Shehu Dan Iya

Wallahi “Yan Fim Din Hausa Sunfi Malamai Tasiri  A Wannan Lokacin.

Malam Shehu Dan Iya ya fara da sallama irin ta addinin musulunci wato Assalamu Alaikum.

Idan mukayi duba da yadda al-ummar mu ta Hausawa ta sauya a lokaci guda zamu fuskanci cewa tabbas “Yan Fim din Hausa na Kannywood Sunfi Malamai kamar yadda wanca nanka ya fada a kwanakin baya.

Babban Dalilin fadin haka shine,Babu wata rana daya da ba’a fito da wani sabon Shiri Wanda Hausawa suke tururuwar kalla.

Idan mukayi la’akari da gidajen talabijin da muke dasu,hakan bai isarwa Hausawa ba,akwai hanyoyi da dama da ake samun shirye-shiryen wato ta irinsu manhajar YouTube da sauransu.

A hakikanin gaskiya ko wacce Al Umma tana Koyi da abunda take gani yau da kullum.

Shi kuwa wa’azi ko karatun Malamai wasu basa saurara sai Shekara -shekara,Kuma acikin kaso 70  cikin 100 na Hausawa sune masu bibiyar shirye-shiryen a koda yaushe,ragowar 30 dinne kadai suke bibiyar Malamai masu karantarwa.

Mene ra’ayin ku game da wannan batun na Malam Shehu Dan Iya?

Www.labarai.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!