Labaran Duniya
Uganda zata rasa babban filin tashi da saukar Jiragen ƙasar sakamakon gaza biyan bashin da ta karɓo daga China shekaru 20 da suka gabata.
Gwamnatin ƙasar Uganda tana gaff da rasa babban tashi da saukar Jiragen sama sakamakon bashi tsakaninta da ƙasar China.
Gwamnatin ta gaza biyan rancen da suka karɓo hakan ne ma ya sanya dole su sallama filin jirgin domin yana daga cikin tsarin yarjejeniyar da ƙasashen biyu sukayi tun da farko.
Filin tashi da saukar jiragen sama mai suna Entebbe shine babba a ƙasar ta Uganda, kuma yana ɗaya daga cikin tsarin yarjejeniyar China da Uganda na karɓar bashi tare da sauran kadarori.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, “Shugaban ƙasar ta Uganda mai suna Yoweri Museveni ya tura wakilai domin sake sauya tsarin yarjejeniyar. Amma hakan bai yiwu domin kuwa China taƙi saurarar wakilan na Uganda.
A shekarar 2015 Gwamnatin ta Uganda ta ƙulla yarjejeniya da Babban Bankin ƙasar China domin karɓar bashin dala biliyan $207 da zummar biya cikin shekaru ashirin alƙawarin da Uganda ta karya.
Www.labarai.com.ng