Labarai

Tubabbun mayaƙan Boko Haram sun gudanar da zanga-zanga a sansanin da ake tsare da su a Jihar Borno. Ko menene dalili?

 

Tsofaffin mayaƙan Boko Haram waɗanda suka miƙa wuya tare da zubar da makaman yaƙi a baya sun fara zanga-zanga a wuraren da aka ajiye su.

Zanga-zangar kamar yadda rahotanni suka tabbatar shine karo na huɗu, kuma babban muƙasudinta shine suna cewa sun gaji da zaman sansanonin da ake tsare da su.

Kamar yadda wasu bayanai suka fito daga Jami’an tsaro masu kula da sansanin da ake tsare da tubabbun ƴan Boko Haram ɗin; Jami’an sun bayyana cewa ba komai ya janyo zanga-zangar ta tsofaffin mayaƙan na Boko Haram ba, face sai kiransu ga Gwamnati akan ta sallame su ko kuma tasan inda zata yi da su, a cewarsu sun gaji da zaman sansanin.

Sun ƙara da cewa, an ajiye su a sansanonin sama da watanni huɗu ba tare da ganin iyalansu ba. Daɗin daɗawa yayin zanga-zangar an tabbatar da tsoffin mayaƙan na Boko Haram sun farfasa waɗansu abubuwa dake a sansanin na garin Maiduguri, Jihar Borno.

Kuma an bayyana cewa, tun a baya waɗansu daga ciki tubabbun mayaƙan na Boko Haram suka tsere ta ɓarauniyar hanya domin sun gaji da zaman sansanin nasu.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!