Labarin Mutuwa
Tsohon Shugaban Sojoji na ƙasa a Jamhuriya ta biyu, mai suna Janaral Muhammad Wushishi ya rasu.
Tsohon hafson Sojoji na ƙasa a zamin Jamhuriyya ta biyu, wato Janaral Wushishi ya rasu.
Iyalansa ne suka tabbatar da hakan, tare da cewa ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a wani asibiti dake birnin London.
Janaral Wushishi an haife shi a Jihar Neja, ya kuma yi aiki a matsayin shugaban Sojoji na ƙasa tsakanin shekarar alif 1981 zuwa alif 1983.
Kuma shine Janar ofisa na sashi na 4 ta rundunar Sojan Nigeria a shekarar 1976 yayinda kuma ya riƙe muƙamin Kwamandan babbar kwalejin Sojoji dake Jaji a shekarar 1979.
Www.labarai.com.ng