Tirkashi Hukuncin Kotu Yasa Wani dan Kwnakwasiyya Ya Yanke Jiki a Jihar Kano

Tirkashi Hukuncin Kotu Yasa Wani dan Kwnakwasiyya Ya Yanke Jiki a Jihar Kano
Cikin jimami muna kan wani matashi ɗan ƙaramar hukumar Kumbotso muna yi masa firfita bayan ya yanke jiki ya faɗi sakamakon ƙwace kujerar Dan Kawu da kotu tayi kafin garzayawa da shi Asibiti, ji kake kwatsam wasu fusatattun matasa sun sauke glass ɗin motar Jagoran ƙaramar hukumar Kumbotso wacce take ɗauke da number hukumar FRSC wadda direban ta ma jami’in wannan hukuma ne.

Cikin fushi matasan suka rinƙa zage-zage tare da cewar ba zai yiwu su tsare akwati, su raka, su jira sannnan Jagorori su zuba ido ana yi musu ɗauki ɗai-ɗai ba, inda wasu suke ikirarin sai sun sauke kowacce bana ta Jagororin jammaiyar tunda sun gaza yin komai.
Mun so zantawa da waɗannan matasa amma damuwar da muma muke ciki ta hana mu kataɓus.
A ƙarshe muna kira ga Jagororin Kwankwasiyya tun daga sama har ƙasa da su farga su tashi tsaye domin akwai damuwa kaji masoyinka yana cewa daga yau ya haƙura da kai saboda yana ganin ba zaka iya kare kanka ba balle shi na ƙasa.
Muna Addu’ar Allah ya dawo mana da kowacce kujera da muka rasa Amin.
Cmrd Nazy Wasna Tarauni
Secretary Kwankwasiyya Reporters Tarauni LG