Labaran Duniya

Taliban ta haramtawa gidajen TV a Afghanistan amfani da mata yan jaridu a matsayin masu gabatar da shirye-shirye ko labarai.

 

Ƙungiyar Taliban sun sake sanar da sabuwar doka tare da shata layi ga shafukan watsa Labarai na Akwatin Talabijin (TV) inda suka gargaɗesu da su daina barin mata suna gabatar da shirye-shirye.

Ma’aikatar gyaran ɗabi’u da daukaka darajar al’amuran wadda take ƙarƙashin kulawar Taliban ta wallafa wannan sanarwa cikin wani shirin Radiyo daya gabata jiya Lahadi. 

Taliban sun gargaɗi cewa ya zama wajibi kowanne gidan Talabijin ya kaucewa yin amfani da mata yayin gabatar da shirye-shirye. 

A baya ma ƙungiyar ta Taliban dake ƙasar Afghanistan ta bayyana cewa duk matan da suke karatu a Jami’o’i ya zama wajibi su rinƙa yin shiga dai-dai da koyarwar addinin Islama.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!