Tsaro

Sojojin Nigeria sun daƙile harin ƴan ta’addan Boko Haram a garin Buni-Yadi dake Jihar Yobe.

 Dakarun Sojin Nigeria, sun daƙile mayaƙan ƙungiyar Boko Haram a yayinda suke yunƙurin kai hari jiya a garin Buni-Yadi dake ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Hakan ne ma ya sanya al’ummar garin suka fara murnar al’amarin.

Jaridar Daily Nigeria ta wallafa cewa dakarun Sojin sunyi artabu da ƴan ta’addan kafin daga bisani su samu nasarar daƙile harin na su.

Har’ilayau; shaidun gani da ido sun tabbatarda cewa ƴan ta’addan sunyi yunƙurin kutsawa cikin garin na Buni-Yadi bisa kan ababen hawa.

Bayan daƙile harin, rundunar Sojin tayi nasarar kashewa tare da ƙwato waɗansu daga cikin makamai mallakin ƴan ta’addan na Boko Haram.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!