Labaran Duniya
Shugaba Buhari yayi tafiye-tafiye sau 130, ya kuma ziyarci kasashe daban-daban har 36.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi tafiye-tafiye sau 130 tare da ziyartar ƙasashen daban-daban har 36 a faɗin Duniya.
Ziyararsa ta ƙarshe zuwa wara shine zuwansa Dubai a farkon watan Dasamba inda ya samu rakiyar Ministoci har guda goma.
Masu kula da al’amuran yau da kullum suna ganin cewa waɗannan tafiye-tafiyen da Shugaba Buhari yayi ba su da amfani ɗari bisa ɗari ga al’amuran da suka shafi siyasa, tsaro da tattalin arziƙin Nigeria.
Www.labarai.com.ng