Labarai

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Harin Da “Yan Bindiga Suka Kai Jihar Kaduna – Labarai.com.ng

 Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da sabbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai Jihar Kaduna da ya yi sanadiyyar kisan mutum 38 da ƙona gidaje da ma amfanin gona a ƙarshen mako.Buhari ya ce kashe-kashen da suka faru a ƙauyukan Kauran Fawa da Marke da Ruhiya na Ƙaramar Hukumar Giwa “sun ɓata mani rai kuma abu ne da ba za a lamunta ba,” kamar yadda sanarwar da Garba Shehu ya fitar ta bayyana.


“Ya (Buhari) sake jaddada umarninsa ga jami’an tsaro da su yi dukkan mai yiwuwa wajen daƙile ayyukan ‘yan ta’adda.”


Kazalika, a cikin makon da ya gabata ‘yan fashin daji sun kashe mutane a ƙananan hukumomin Zangon Kataf da Chikun da Birnin Gwari da Igabi da Kauru, dukkansu a Jihar ta Kaduna.


Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa da kuma ‘yan Najeriya ga gwamnatin Kaduna sannan ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan su.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!