Uncategorized

Shugaba Buhari ya gana da ƴan wasan Nigeria, gabanin karawarsu da ƙasar Tunisia.

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ƙarfafawa ƴan wasan Nigeria gwiwa bisa ga wasan Kofin Afrika da yake gudana a Kamaru.

Buhari ya isar da saƙon ne a yayin wata tattaunawar bidiyo ta musamman da yayi da ƴan wasan gabanin karawarsu da ƙasar Tunusia a daren yau.

Yayi da yake magana daga fadarsa ta Villa, Buhari yayi magana da mai horas da ƙungiyar ta Super Eagles Augustine Eguavoen, Ahmed Musa, Shugaban hukumar ƙwallon kafa ta Nigeria Pinnick Amaju da kuma Ambasadan Nigeria dake Kamaru mai suna Janar Abayomi Olinisakin.

Buhari ya sake miƙa roƙo ga ƴan wasan na Super Eagles, akan su cigaba da farantawa ƴan Nigeria rai, tare da samun nasarar lashe Kofin na Afirka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!