LABARINA
Trending

Shin Shirin LABARINA yazo karshe kenan? Masoya na kewar jaruma Nafisa Abudullahi

Tun bayan da fitacciyar jarumar Kannywood Nafisa Abudullahi ta bayyanawa duniya cewa bazata sami damar cigaba da daukar cigaban shirin fim din LABARINA ba,labarin ya karade shafukan sada zumunta harma da inda ba’a zata.

Mutane da dama musamman masoyan shirin mai farin jini na Labarina sun bayyana rashin jin dadin su akan hakan.

Sai dai wasu suna ganin fitar Sumayya daga cikin shirin zai nakasa LABARINA din,a yayin da wasu suke ganin ai dama an gina labarin ne akan Jarumar Nafisa Abudullahi.

Nafisa Abudullahi din a kankin kanta ta bayyana cewa dalilin dayasaka bazata fito ba shine saboda tana son samun lokacin kanta dana masana’antar kayan kwalliyar data fara sannan kuma dana finafinan da take bukatar kamfanin ta ya fara dauka,taci gaba da fadin dole shirin zasu cigaba koda babu ita.

Haka dai mutane sukaci gaba da bayyana ra’ayoyin su daban daban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!