Uncategorized

Shekarau bashi da amfani a APC, sau ɗaya ya taɓa tallafawa Jam’iyyar da naira dubu ɗari. ~Inji Abdullahi Abbas

 

Shugaban Jam’iyya APC a reshen Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya zargi Sanata Ibrahim Shekarau da cewa kansa-da-iyalansa kawai yake taimakawa tun bayan ɗarewarsa kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a 2019.

Abdullahi Abbas ya bayyana cewa loƙaci ɗaya da Sanata Shekarau ya taɓa tallafawa Jam’iyyar ta APC shine loƙacin watan Azumi da ya bayar da dubu ɗari 100,000؟

Abdullahi Abbas ya cigaba da iƙirarin cewa, Allah ne ya taimaki Shekarau ya zama Gwamna amma da sanadiyarsu, domin har miliyan 3 suka tallafa masa da shi domin sayan takardar neman takara. Ƙuma sun taya shi yaƙin neman zaɓe da duk irin gudunmawa, amma abin takaici yanzu daga shi sai iyalansa ne suke jin ɗaɗin mulkinsa.

Shugaban Jam’iyyar ta APC ya kuma ƙara da cewa ƙofa a buɗe take ko yaushe Shekarau ya shirya barin Jam’iyyar tare da shiga Kwankwasiyya dama can shi “kara da kiyashi” ne.

A shekarar 2003, Buhari ya taimake shi ya zama Gwamna a Ƙano amma daga ƙarshe yaci amanarsa. Don haka yanzu ma baza muyi mamaki don ya butulce mana ba.

Kamar yadda Jaridar Sahelian Times ta wallafa; Abdullahi Abbas ya bayyana hakane a jiya yayin tattauna da gidan radiyon ƙasa-da-ƙasa (IRS).

A ƙarshe, Abdullahi Abbas ya ƙaryata zargin cewa sun yi watsi da Shekarau ɗin, tare da bayyana cewa duk loƙacin da buƙatar ganinsa ta bijiro, koda an sanar masa sai yace yana ƙasar waje.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!