Labaran Kannywood

Shekara kwana: Yadda Halima Atete da mijin ta suke murnar cikar su shekara daya da Aure

Tsohuwar fitacciyar jarumar Kannywood Halima Atete jarumar data yi fice a masana’antar Kannywood tare da mijin ta suna murnar cikar su shekara daya da aure (1 year wedding anniversary).

Jarumar ta wallafa hotunan su a shafin ta na sada zumunta dake Instagram.

Mutane da dama ne suka taya ta murna tare da addua’r daurewar zaman lafiya a gidan nasu.

Halima Atete tare da mijin ta

Ga kadan daga cikin comments din mutanen harma da tsoffin abokan sana’ar ta.

Abdallah Amdaz yace “Allah ya karo shekaru masu Albarka”. Nan take Halima din tace Amin.

Nazifi Asnanic yace  “Masha Allah”

Aishatul Humaira tace “Happy Anniversary Masoyiya ,Allah ya kara zaman lafiya ya kawo zuri’a dayyiba”

Hafsat Idris tace “Allah ya kara zaman lafiya”

Haka dai mutane suka ci gaba da taya ta murna tare da musu addua’r daurewar zaman lafiya.

Muma ma ana mu ɓangaren,muna taya su murna da addua’r Allah ya kawo kazantar daki Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!