Labaran Duniya

Shatu Garko: Itace Tafi Kowacce Mace Kyau A Najeriya A Shekarar 2021

 Shatu Garko itace macen datafi kowacce mace kyau a Najeriya a shekarar 2021.

Shatu Garko, mai shekara 18, ta doke zaratan mata 18 a bikin da aka gudanar ranar Juma’a da dare a Landmark Centre da ke birnin Legas.Shatu ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turance.


Nicole Ikot ce ta zo ta biyu, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku.

Ta karɓe kambin ne daga hannun Etsanyi Tukura ‘yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a 2019.

A cewar masu shirya gasar, wadda ta yi nasara za ta samu kyautar kuɗi naira miliyan 10, da zama a gidan alfarma na shekara ɗaya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.

Wacece Shatu Garko?

Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 44, Shatu Garko ‘yar asalin Jihar Kano ce kuma ita ce ta wakilci yankin arewa maso yammacin ƙasar.


Taƙaitaccen tarihinta da aka bayar a wurin gasar ya nuna cewa tana da shekara 18 da haihuwa, kuma mai tallan hijabi ce da ke ƙaunar hawa doki.


Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!