P-Square reunion
Shahararrun Mawakan Kudu P-Square Sun Bawa Duniya Mamaki Ganin Yadda Suka Shirya
Fitattun “Yan biyun mawakannan a Najeriya Peter and Paul da aka fi sani da P-Square sun sanar da cewa sun shirya a yau.
P-Square sun ce sun shirya tsakaninsu, bayan wani rikicin cikin gida da ya raba kansu a shekarar 2017 wanda har yanzu ba’asan musabbabin rabuwar ba.
A shekarar 2015 P-Square suka lashe kyautar mawaka mafi shahara a bikin MTV Africa da aka gabatar.
To amma duk da sun shirya ‘yan biyun basu bayyana ko za su sake fito da sabon kundi wakoki tare ba har yanzu.
Sai dai masoyansu na fatan su rera musu sabbin Zafafan wakoki tare, kamar yadda suka yi fice da wakoki kamar ‘Do me’ da ‘Chop My Money’ ,’Bizzy Body’ da Kuma Personally.
Mene fatan ku game da hadewar shahararrun mawakan biyu?
Www.labarai.com.ng