Labaran Duniya

Sanata Ahmed Lawan ya buƙaci ƴan Nigeria kan su cigaba da taimakon Sojoji da addu’o’i a yayin da suke yaƙar ƴan ta’adda.

Shugaban majilisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan yayi kira ga ƴan Nigeria akan su cigaba da ƙarfafawa dakarun Sojojin Nigeria gwiwa da addu’o’i a yayin da suke ƙoƙarin shawo kan matsalar tsaro.

Ahmed Lawan, ya bayyana hakan ne a jiya bayan gudanar da sallar Juma’a a babban masallacin birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa, “alhakin ƴan Nigeria ne su taimaki dakarun Sojoji da addu’a domin ƙara samun nasarar tabbatarda tsaro”.

Ya kuma ƙara da cewa, “Majalisun da suke wakilta, za su cigaba da aiki tuƙuru wajen samar da kayan yaki domin ƙarfafa Sojojin na Nigeria.

A ƙarshe ya yabawa Sojojin na Nigeria musamman irin yadda suke sadaukar da rayuwakansu domin kare Nigeria da kuma yaƙar ayyukan ta’addanci a Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!