Labaran Siyasa

Rikici Ya Kare: Ganduje Ya Jewa Kwankwaso Ta’aziyya A Yau – Labarai.com.ng

 Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya je yi wa tsohon gwamna kuma babban abokin hamayyarsa Rabiu Musa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar ɗan uwansa.Gwamnan ya isa gidan Kwankwaso na Miller Road da tsakar ranar yau Talata, inda suka ziyarci ƙabarin mahaifin Kwankwaso da ya rasu a baya.

A ranar Litinin ne Inuwa Musa Kwankwaso, wanda ƙani ne ga Rabiu, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Ya rasu yana da shekara 64.

Alaƙa tsakanin shugabannin biyu ta daɗe da lalacewa tun bayan da Kwankwaso ya miƙa wa Ganduje ragamar mulkin Kano a 2015 bayan sun shafe shekara takwas a matsayin gwamna da mataimaki. har ta kai ga yanzu Kwankwaso ya koma jam’iyyar adawa ta PDP.

Sai dai Gwamna Ganduje na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida a jam’iyyarsu ta APC tsakaninsa tawagar tsohon gwamna kuma sanata a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau.


Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!