PDP zata maka Gwamnatin Jihar Zamfara a kotu bisa tsige mataimakin Gwamna, Mahdi Aliyu

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tana shirye-shiryen ƙalubalanci dalilin da ya sanya aka tsige Alhaji Mahdi Aliyu a matsayin mataimakin Jihar Zamfara.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne cikin wani jawabi da sakataren Jam’iyyar ta fannin al’amuran da suka shafi labarai mai suna Mista Debo Ologunagba ya bayyana a babban birnin tarayya Abuja.
Sakataren ya bayyana cewa babu dalilin tsige mataimakin Gwamnan na Jihar Zamfara a shari’ance.
Ya kuma bayyana a madadin Jam’iyyarsu ta PDP tsige mataimakin Gwamnan a matsayin wani yunƙuri ne na karya dokokin da ƙasa ta tanada.
Sakamakon haka ya alƙawarta cewa PDP da al’ummar Jihar Zamfara ba za su aminta da ɗanyen hakuncinba.
A ƙarshe ya bayyana cewa, sun kammala duk wani shiri domin ƙalubalantar hukuncin da akayi na tsige mataimakin Gwamnan.