Wasanni
Nigeria ta lallasa Sudan daci 3-1.

Kungiyar Super Eagles ta Nigeria ta lallasa takwararta ta ƙasar Sudan daci 3-1 a wasan neman gurbin shiga zagaye na 16 a login Nahiyar Afrika dake gudana a Kamaru.
Ɗan wasa Chikwueze shine ya fara zura ƙwallon farko a minti uku da fara wasan, kafin Owoniyi da Simon su kara ta biyu da ukun.
Ƙungiyar kasar Sudan ta samu nasarar zura ƙwallonta ɗaya ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
A yanzu dai Nigeria ta samu nasarar shiga zagaye na 16 a gasar.