Labarai

Nigeria na bisa hanyar zama jagaba a fannin kasuwanci a Afrika. ~Cewar Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Nigeria ce ƙasar da akafi sha’awar a buɗe kasuwanci a nahiyar Afrika.

Ya ce Nigeria tana bisa hanyar zama jagaba ta fannin cigaban kasuwanci da masana’antu.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi na musamman a taron harkokin kasuwanci da ya gudana jiya Asabar a Dubai.

An shirya taron ne tsakanin sashin kasuwancin Nigeria da ƙasar Saudi Arabia tare da haɗin gwiwar ma’aikatar masana’antu da zuba jari ta Nigeria.

A gefe guda kuma, mai magana da yawun Shugaban ƙasa wato Mista Femi Adesina, ya ƙara da cewa Shugaba Buhari yana ƙoƙarin ganin al’amura sun dai-daitu yadda ya kamata a Nigeria ta hanyar ƙarfafa fannin kasuwanci.

Ya kuma yi biyanin yadda Nigeria ta kasance ƙasar da tafi jan hankalin masu zuba jari a nahiyar Afrika.

Har’ilayau, Shugaba Buhari ya rufe da cewa Gwamnatinsa zata cigaba da bijiro da tsaruka waɗanda za su rinƙa taimakawa baƙi masu zuba jari a Nigeria.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!