Labaran Kannywood
Neman Saurayi a Twitter ya jawa Amal Umar maganar iskanci a wajen “yan Twitter

Fitacciyar jaruma a cikin masana’antar Kannywood Amal Umar ta bayyana a shafinta na Twitter cewa “Tana bukatar saurayi” bayan hakan ne da wuya ai kuwa Matasan kafar Twitter din suka dinga fadawa jarumar maganganu marasa kan gado da kuma da’a a cikin su.
Daman ba wannan ne karon farko da ake yiwa Jaruman ta masana’antar Kannywood din haka ba,domin ko a baya ansha yiwa jarumai irin su Rahama Sadau da kuma Hadiza Gabon hakan,ba tare da bata lokaci ba zamu kawo muku bidiyo akan hakan wanda tashar Duniyar Kannywood dake kan manhajar YouTube sukayi cikakken bayanin da bamuyi ba a sama.