NECO: Yadda Zaku Duba Sakamakon Jarrabawar NECO
NECO: Yadda Zaku Duba Sakamakon Jarrabawar NECO ta shekarar 2021
Da fari idan mutum zai duba sakamakon jarrabawar NECO wato result zai mallaki abunda ake kira da ‘scratch card’.
Bayan ka mallaka zaka shiga cikin shafin yanar gizo-gizon jarrabawar NECO din,shafin shine kamar haka;
http://www.mynecoexams.com/results/default.aspx
Bayan ka shiga zasu bukaci ka saka cikakken bayananka wato wanda ya hada da sunanka,da kuma lambar jarrabawar taka wadda ake kira a turance ‘Examination number’ ,bayan ka sakasu baki daya zasu bukaci ka bayyana shin NECO din a Makarantar gwamnati kayi jarrabawar ko kuma a makaranta mai zaman kanta.
Duka saika zabi daya daga cikin wadda akayi.
Anzo karshe sai katafi zuwa gaba wato ‘Next’ kana kammalawa zasu bayyana maka sakamakon jarrabawar NECO din dakayi.
Daga nan zaka iya saukeshi wato ‘download’
Izuwa cikin Wayarka ya zamana ya zama PDF wanda wasu suke kira da soft copy a turance baki daya.