Labaran Kannywood
Trending

Naziru Sarkin Waka Yayi Kaca-Kaca Da ‘Yan Kannywood Akan Ladin Cima

Fitaccen mawakin nan kuma jarumi a cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood ya fito yayi Allah wadai da abunda wasu jarumai sukayiwa fitacciyar jarumar nan wadda taga jiya kuma taga yau a cikin masana’antar Kannywood din wato Ladin Cima.

Naziru din ya fito karara ya ambaci sunayen manyan Kannywood guda biyu wanda suka hada da Ali Nuhu da kuma Falalu A Dorayi ya kara da cewa in har ba gaske bane maganar Ladin Cima cewa ana bata dubu biyu dubu uku su fito suce ba haka bane mana,haka dai ya dinga zayyano abunuwan da dai sai Wanda ya gani kadai zaiyi Alkalanci.

Jarumar dai ta bayyana ne a cikin wani shiri da gidan jaridar BBC Hausa suke gudanarwa wanda sukayiwa lakabi da Daga Bakin Mai Ita,jarumar a cikin hirar ta kusan mintuna shida zuwa bakwai ta bayyana halin da take ciki da kuma irin mawuyacin halin data kusa shiga dabadan Allah ya kawo mata dauki ba.

Labarin dai ya dauki hankulan mutane sosai da sosai wanda ake ganin to ta ina ne sauran jaruman musamman ma masu ragowar karfi suke samun kudaden shiga bayan na masana’antar?

Zaku iya kallon cikakken tsokacin da Naziru Sarkin Wakar yayi anan kasa,kada ku manta ku bayyana mana ra’ayoyin ku a kasan wannan labarin.

YouTube/c/GimbiyaTV

https://youtu.be/OpHrbhC5jaY

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!