Labarai

Nan bada jimawa ba zamu shafe labarinku. ~Buhari ya gargaɗi ƴan Bindiga

 Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da kisan mutane wanda akayi kwanakin baya a ƙauyen Goronya dake ƙaramar hukumar Illela ta Jihar Sokotto.

Kamar yadda ya saba ayyanawa, a wannan karon ma Buhari ya bayyana cewa Gwamnatinsa zata sanya ƙafar wanda ɗaya da ƴan ta’adda da ƴan Bindiga.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya wallafa, “ya sake yin alƙawarin cewa Gwamnatinsa baza ta zuba akan irin ta’addancin da yake faruwa a sassan Nigeria ba.

Wajibi ne a yi amfani da ƙarfin Jami’an tsaro wajen murƙushe ƴan ta’adda a Nigeria. Domin kashe-kashen da ake na mutane bazai wuce a banza ba, suma sai sun ɗanɗana.

Ya kuma ƙara da cewa, “Gwamnatinsa tana cigaba da bin matakan inganta dakarun yaƙin ƙasar ta Nigeria domin samun damar murƙushe ƴan ta’adda.

A ƙarshe Buhari ya bayyana cewa, Gwamnatinsa baza ta zuba ido tana ganin ƴan ta’addan suna cin karensu babu babbaka ba, wanda hakan ne yake tilastawa miliyoyin mutane tsoron fita neman abinda zasu ci da iyalansa.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!