Labarin Mutuwa
Trending

Mutuwar Dr Ahmad BUK Ta Girgiza Duniya Baki Daya,Allah Yayi Mishi Rasuwa A Yau Ne

Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana ya rasu a yau Juma’a.

Wata jikarsa ta tabbatar wa da BBC Hausa labarin rasuwar.

Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.

Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, kuma ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani kan labarin.

Mun sami labarin ne daga BBC Hausa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!