Uncategorized

Mutane su daina barin Malamai suna amfani dasu domin biyan bukata a wajen yan Siyasa.~Cewar Sheikh Maqari

 Shehin Malamin ya bayyana cewa talakawa su daina bari kwaɗayayyun Malamai suna amfani dasu wajen neman kuɗi, kuma suna umaratarsu su zaɓi ƴan Siyasa.

Maƙari ya bayyana haka ne cikin wani gajeran faifan bidiyo nasa da yake yawo a kafafen sada zumunta.

Ferfesan ya ƙara da cewa, Duk Malamin da ya kawo muku tallar wani ɗan siyasa, to ku ce masa ya rantse da Al-Qur’ani akan ba kuɗi aka bashi ba, kafin ku yarda da shi.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!