Labaran Duniya

Muna takaici bisa ga irin halayyar da Buhari tare da wasu Gwamnoni suke nunawa akan rashin tsaron Arewa. ~A cewar kungiyar ACF

 Kungiyar gamayyar Arewa ta bayyana takaicinta bisa ga halin ko in’kula da Gwamnonin Arewa suke nunawa duk da irin kashe-kashen da ƴan ta’adda suke yi a yankin na Arewacin Nigeria.

Wannan ya fito cikin wata takarda ta musamman da sakataren ƙungiyar ta ACP mai suna Emmanuel Yawe ya bayar ga ƴan Jaridu yau Lititin a garin Kaduna.

Takardar tana ɗauke da cewa, “abin takaici ne duba da irin halin ko in kula da Gwamnonin Arewa tare da Shugaban ƙasa suke nunawa duk da irin ta’annatin da ake tafkawa a Arewa.

A cewar gamayyar ƙungiyar ta Arewa, “bayan Gwamna Zulum, babu wani Gwamna harda Shugaban ƙasa da ya damu akan ya ziyarci wuraren da iftila’in ta’addancin ƴan ta’adda ya shafa.

A ƙarshe sun bayyana takaicinsu bisa ga yadda ayyukan ƴan ta’adda kullum yake ƙara ta’azzara a Arewacin Nigeria.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!