Videos
Mr LECTURER (Full Movie) by Deezell

Mr LECTURER sabon shiri ne da mawakin Hausa Hip-hop dinnan Deezell ya shirya kuma ya bayyana a ciki,shirin yayi matukar bada ma’ana,sannan ya kara fito da abubuwa da dama wadanda ba’a yin su a cikin masana’antar Kannywood.
Shirin anyi shi ne Engausa (Hausa da Turanci) wanda duk wani Dan Najeriya idan ya kalla zai fahimce shi a duk inda yake.
Shirin ya hada da jarumai da mawaka kamar haka a ciki;
- Ali Nuhu
- Soja Boy
- DJ AB
- Deezell
- Dabo Daprof
- Feezie
- Maddox
- LS Vee
- Cdeek
Da sauran jarumai da mawaka a ciki, shirin idan ka kalla zaka so ace akwai cigaban shi bayan sakin sa da akayi a karon farko.
Kada mu cika ku da surutu,zaku iya kallon cikakken shirin na Mr Lecturer anan kasa,kada ku bari a baku labari.