Minista Rauf Aregbesola ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari tana samun nasarori ta fannin magance tsaro.
Tsohon Gwamnan Jihar Osun kuma Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa an baiwa Jami’an tsaro dukkan dama domin magance matsalar tsaro tare da daƙile hare-haren masu ƙoƙarin dagula al’amura a Nigeria.
Ya bayyana haka ne a yayin ganawa da ƴan Jaridu yayin wani taron hukumomin tsaro daya gudana jiya a fadar Shugaban ƙasa dake babban birnin tarayya Abuja.
Mista Aregbesola ya ƙara da cewa, “duk da ana samun nasarori a yaƙi da ƴan ta’adda, Gwamnatinsu baza ta gajiya wajen tabbatar da tsaro a faɗin Nigeria ba.
Kamar yadda aka gudanar da taron Shuwagabannin tsaro ƙarƙashin Jagorancin Shugaba Buhari, na tabbata cewa ƴan Nigeria za su ga sauyi game da ƙoƙarin Jami’an tsaro na magance ayyukan ta’addanci a Nigeria.
Bayan tambayar Aregbesola dangane da irin shirinsu na daƙile sace-sace musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna?; Ministan ya tabbatar da cewa an samar da Jami’an tsaro na musamman waɗanda za su rinƙa shawagi domin domin daƙile ayyukan ƴan bindigar da suka addabi yankin.