Wasanni
Messi ya zama gwarzon Ɗan wasan Duniya a karo na 7.
Shahararren tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona mai taka leda yanzu a ƙungiyar PSG wato Lionel Messi shine ya lashe kyautar gwarzon Ɗan wasan kƙwallon ƙafa na Duniya a shekarar 2021.
Sai dai nasarar ta Lionel Messi tana cigaba da jawo cece-kuce tsakanin magoya baya da masu sharhi a fannin wasan ƙwallon ƙafa inda wasu suke ganin Ɗan wasan Bayern Munich wato Robert Lewandowski ne ya cancanta ya lashe kyautar duba da irin rawar daya taka a kakar wasa data gaba.
Har’ilayau, Messi shine Ɗan wasan da ya jagodanci ƙasarsa ta Argentina izuwa lashe gasar Kofin America ta Kudu (Copa America) wanda tsawon shekaru 28 ƙasar ta gaza lashewa sai bana.
Www.labarai.com.ng