Uncategorized

Matasan Arewa sun jaddada goyon bayansu ga Osibanjo a yunƙurinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Ƙungiyar matasan Arewa daga jihohi 19 ƙarƙashin tutar “North-4-Osinbajo” sun nuna goyon bayansu a yunƙurin da Osibanjo yake na fitowa takarar Shugaban ƙasa.

Babban shugaban ƙungiyar mai suna Sani Mohammed shine ya bayyana haka yayin wani taro da suka haɗa a garin Jos.

Mohammed ya bayyana cewa kowa yana da damar zama mamba a cikin ƙungiyar ba tare da bambancin aƙida, addini, ko kuma yare ba, fa ce sai domin nuna goyon baya ga mataimakin shugaban ƙasar, Furofesa Yemi Osinbajo a ƙoƙarinsa na ganin ya fito takarar shugabancin Nigeria.

A cewarsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayarda gagarumar gudunmawa ta ɓangaren cigaban tattalin arziƙi, sannan yana da yaƙinin zai zama abin alfahari idan aka bashi dama ya zama shugaban Nigeria.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ƙungiyar North-4-Osinbajo an ƙirƙire ta ne musamman domin yaƙin neman zaɓen muƙaddashin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!