Labarai

Matasan Arewa sun ƙirƙiri sabuwar ƙungiya mai suna YOCAD domin ceto Arewa daga halin da take ciki.

ABIN DA YA KAMATA KU SANI DANGANE DA SABUWAR KUNGIYAR MATASAN AREWA, YOCAD.

An ƙirƙiri ƙungiyar matasa masu burin ceto Arewa, YOCAD, a ranar 10 ga watan Janairu 2022. Hakan kuma ya tabbata ne biyo bayan shawarwari daga ɓangarorin masana, matasa da kuma dattawa don samar da ƙungiyar da zata fito gaba-gaɗi domin samar da cigaba, zaman lafiya da rayuwa mai kyawu ga al’ummar Arewa.

Babban muƙasudin ƙirƙirar wannan ƙungiya shine domin wayarwa da al’ummar Arewa kai musamman mazauna yankunan karkara game da manufar zaɓe, ma’anar zaɓe da kuma amfanin zaɓe ga cigaban rayuwar al’umma.

Sanin kowa ne cewa Arewa muna cikin wani hali, kuma wannan yana tattare da zaɓar gurɓatattun shuwagabanni. Abin takaicin shine, waɗansu mutanan suna zaɓe ne kawai ba tare da sanin wanda suka zaɓa ba, ko kuma matsayin zaɓen ga walwala da cigaban rayuwarsu.

Arewacin Nigeria, yanki ne da Allah Ya albarkace mu da yawan al’umma masu siƙira, ma’adanai, masana’o’i, harkar noma, kiwo da sauran harkokin kasuwanci; sai dai haryanzu mun rasa zaman lafiya sakamakon riƙon sakainar kashi da wakilanmu suke mana.

A wannan karon matasa maza da mata sun amsa kira. Sun yarda da cewa suna da loƙaci, hikima da kuma damar aiwatar da wani abu domin samun zaman lafiya, cigaba da walwala a yankinmu mai albarka.

Kofa a buɗe take ga duk wanda yake da dama, hali ko ikon bayarda gudunmawa domin tafiyar da al’amuranmu cikin nasara.

Muna da wakilai daga Jihohi 19 tare da babban birnin tarayya Abuja waɗanda za su rinƙa bayarda tasu gudunmawar ƙarƙashin ƙungiyar YOCAD a matakin Jihohi, ƙananan hukumomi zuwa lunguna da saƙo na Arewacin Nigeria.
Kuzo mu ceci Arewa!

Zaku iya bibiyar kungiyar YOCAD ta shafukan sada zumunta kamar haka;

Facebook: Youths Coalition for Arewa Deliverance
WhatsApp: +2348068832474
Twitter: @Yocad4Arewa
Gmail: [email protected]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!