Tsaro

Masu garkuwa da mutane sun buƙaci a basu miliyan 200 cikin awanni shida bayan sun sace wani tsohon Ɗan sanda a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ƴan bindigar da suka kama tsohon ma’aikacin hukumar ƴan Sanda a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun bayarda adadin awa shida akan a kawo miliyan 200 kuɗin fansa.

Mutumin da aka kama mai suna Dambo Hosea yana daga cikin gungun mutanen da ƴan Bindigar suka sace a ranar Lahadi bayan da kuma suka kashe tsohon ɗan takarar Gwamnan Jihar Zamfara mai suna Sagiru Hamidu.

Bayan sun kirawo iyalan Ɗan sandan, ƴan Bindigar sun shaida musu cewa su hanzarta kawo kuɗin fansar kafin su ɗauki mataki a kansa.

Bayan haka ne kuma iyalan suka shiga roƙon ƴan bindigar akan cewa miliyan 2 za su iya biya, lamarin da ya tunzura ƴan bindigar har suka katse waya.

Har’ilayau, yayin tattaunawa da iyalin mutumin, ɓarayin sun haɗa shi magana da iyalan nasa ta wayar salula, yayinda ya roƙe su cewa su taimaka su baiwa ƴan bindigar kuɗin da suka buƙata duba da irin yanayin da suka jefa shi.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!